Magana Ta Lalace, Buhari Ya Fada Tarkon Makiya~Inji Alh. Abdulkareem Dayyabu..

Najeriya Ta Fada Tsaka Mai Wuya, Gaba Siyaki Baya Damisa__Inji Alh. Abdulkareem Dayyabu.

Abdulkareem dayyabu yace, magana ta lalace, Buhari ya fada tarkon makiya, kodai mu kwato Muhmammadu Buhari daga hannun su a samu zaman lafiya ko kuma su raba shi da Allah, su raba shi da kowa, kowa yayi takansa, daga lokacin da ‘yan uwanka na jini sukayi tarayya da makiyanka, makiyan Allah, makiyan bayin Allah amma ka nuna kai kafi amincewa dasu fiye da kowa, baka neman kowa ko sauraren kowa sai su da wadanda suka hada kai dasu har kowa ya gane haka, to duk wanda yace zai dogara dakai to gaskiya shine yake yaudarar kansa.

Tattalin Arziki da tsaro da siyasa duk sun rushe, babu Wanda yasan inda aka dosa, daga barayin gwamnati sai bokaye sai yan kungiyar asiri da fajirai sune kadai suke amfana da bala’in da ake ciki, wadanda duk yawansu gaba daya basu wuce miliyan 5 zuwa 10 ba acikin mu miliyan 200 ko fiye, amma suna nema sufi karfin mu saboda mun dakata tasu.

Yanzu mafiya yawancin masu laifukan da sukafi na wancan lokacin suna nan Najeriya, wasu ma suna kewaye dashi. Duk Duniya babu kasar da aka taba samun wanda bashi aka zaba ba kuma ko yakin neman zabe bai taba zuwa ba amma yafi shugaban kasa karfin iko sai a wannan mulkin na Buhari.

Kadan daga cikin bayanan Alh. Abdulkareem dayyabu kenan, Ku biyo mu.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published.