Magidanci Da Iyalansa Sun Rasu Sakamakon Rugujewar Gidansu A Kebbi.

Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un! Allahu-akbar!! Bawa baya wuce lokacinsa.

A daren Jiya ne Allah ya Karbi rayuwar Wani Magidanci tare da Iyalansa a Kauyen Yaldu Cikin karamar hukumar Mulki ta Arewa Local government, Wato Kangiwa, A jahar kebbi.

Sun Rasu Ne Sakamakon Faduwar ginin da suke Ciki lokacin da ake tsaka da sharara ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Kuma tuni aka gudanar da Jana’izarsu kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya karbi Shahadarsu, Kana mu da muke a raye idan tamu tazo Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.

Daga Alhaji Hassan Mai-waya Kangiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.