Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa game da rasuwar mahaifin tsohon Gwamna Kwankwaso, Alhaji Musa Saleh, Hakimin Madobi.
A wani sakon da ya aike a ranar Juma’a, Shugaba Buhari ya ce “tare da rasuwar Musa Saleh, mun rasa daya daga cikin tsofaffinmu kuma mafi kyaun sarakunan gargajiya a kasar nan wanda ba za a manta da irin gudummawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da hadin kai ba ko da kuwa bayan rasuwarsa.”
A cewar Shugaban, “Marigayi Saleh mutum ne mai halayyar kirki wanda tawali’u da saukin kai ke cikin manyan halayen sa.
“Bari na yi amfani da wannan damar domin mika ta’aziyata ga tsohon Gwamna Kwankwaso, da Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Masarautar Kano game da rasuwar Hakimin. Allah ya gafarta masa kurakuransa kuma ya saka masa da kyawawan ayyukansa da Aljannah, amin,” Shugaba ya kammala.
Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa
(Kafofin watsa labarai & Jama’a)
Disamba 25, 2020