Mahara Sun Sake Kai Farmaki Jihar Kaduna Inda Suka Kashe Mutum Biyar, Cewar Samuel Aruwan

Rahotannin tsaro daga jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar wasu mutane biyar a wasu sassan jihar, an bayyana cewa, mutanen sun mutu ne a wasu hare-hare daban-daban na ‘yan bindiga a yankin

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ne ya bayyana faruwar lamarin
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyar a kananan hukumomin Zango-Kataf da Giwa a ranar Litinin, jaridar Punch ta ruwaito.

Kwamishinan a baya cikin wata sanarwa ya ce mutane biyu; uba da da, Joshua Dauda da dansa mai shekaru bakwai, Philip, a kauyen Wawan an kai musu hari a karamar hukumar Zangon-Kataf.

Duk da haka, yayin da yake sabunta rahoton, kwamishinan ya ce karin gawarwakin biyu jami’an tsaro sun gano su.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

0 thoughts on “Mahara Sun Sake Kai Farmaki Jihar Kaduna Inda Suka Kashe Mutum Biyar, Cewar Samuel Aruwan

  • April 14, 2021 at 4:23 am
    Permalink

    Karyan ka mungu, na says buhu akan #3,850, ta yaya zaka CE #2,500 ? Haba mallam aji soron Allah fa

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *