Labarai

Mai Mala Buni ya tarwatsa tsarin Gwamna bello ya dawo Fani femi kayode cikin Kwamitin gudanar da babban zaben Jam’iyar.

Spread the love

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sake jaddada matsayinsa na shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, ya sauya matakin da gwamna Abubakar Sani Bello na Neja ya dauka, wanda ya jagoranci jam’iyyar na wucin gadi.

A ranar 9 ga watan Maris ne Mista Bello ya amince da jerin sunayen kananan kwamitocin jam’iyyar na kasa wanda ya cire sunayen Mista Buni da aka zaba, ciki har da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da kuma sauya mukamai da aka bai wa daidaikun mutane.

Bello ya nada Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban kwamitin da’a. Ya kuma nada ministan yada labarai Lai Mohammed a matsayin mataimakin shugaban riko Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin shugaban kwamitin kudi.

Mista Buni ya sauya mukaman gwamnan Neja, inda ya maido da daidaikun mutane kan mukaman da suke rike da su a baya.

A yanzu Mista Sanwo-Olu zai jagoranci kwamitin yada labarai tare da Mista Fani-Kayode a matsayin mataimakin shugaba da kuma Mista Ganduje a matsayin shugaban kwamitin karrama ‘yan sa kai, jami’an diflomasiyya, ‘yan kasashen waje da masu sa ido.

A baya dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa gwamnonin jam’iyyar APC, inda ya umarce su da su kyale Mista Buni ya gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa Gwamna Atiku Bagudu, shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba a ranar 16 ga Maris.

Mista Buhari ya dage cewa taron ya tafi kamar yadda aka tsara a ranar 26 ga Maris. Ya yi gargadin cewa maye gurbin Mista Buni zai iya haifar da matsala kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta dakatar da dukkan ayyukan APC.

Wasikar Mista Buhari ta biyo bayan rikicin mulki ne tsakanin Mr Buni da Bello.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button