Majalisa Ta Gayyaci Ministar Kudi da Akanta Janar Kan Zurarewar Kudi Har Kimanin Biliyan 7.5 Daga Asusun Gwamnati.

Majalisar tace ta Mun gano an cire Biliyan 7.5 daga Asusun Gwamnati a Boye, Ku zo ku mana baya.

Kwamitin majalisar tarayya dake kula da yanda ake kashe kudin Gwanatin ya gayyaci ministar kudi da babban Akanta janar na tarayya dan su yi bayani kan wasu kudi har Biliyan 7.5 da aka cire daga wani asusun gwamnati na musamman.

An cire kudin ne a asirce kamar yanda babban Odita janar na tarayya ya bayyana a cikin Rahotonsa.

Rahoton dai yace an rika cire kudinne a hankali wanda har suka taru suka yi yawa kafin majalisar ta lura da zurarewar kudaden.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *