Majalisar dattijan Nageriya na Shirin zartar da dokar kawo karshen ta’addanci ~Shirin Sanata Uba Sani

Sanatan kaduna ta tsakiya Malam uba sani Ajiya Litinin ya halarci Zama domin tabbatar da tsaro ta Hanyar Kwaskwarima a tsarin makamai a Nageriya Sanatan ya fitar da sanarwa a Shafin sa na Twitter Yana Cewa na zauna da Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai kan harkokin shari’a, ‘yancin dan adam da lamuran shari’a, rundunar sojan ruwa da na safarar jiragen ruwa a yau sun sami nasarar sauraron ba’asin jama’a game da Dokar Bindigogi na (Kwaskwarimar 2021 BILL.

Taron ya samu halartar jama’a da dama Haka ma Shugaban Majalisar Dattawan ya samu wakilcin Sanata Ajayi Boroffice, Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar. An fitar da mahalarta daga manyan jaruman hukumomin tsaro na kasar, da masana harkokin shari’a da tsaro da kuma masu fafutuka na kungiyoyin farar hula. An gabatar da jawabai a wurin jin ra’ayoyin ne daga rundunar Sojojin Najeriya, da Sojojin Saman Najeriya, da Sojojin ruwa , da Hukumar Kwastam, da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya da kuma Hukumar sake fasalin Dokokin Najeriya. Inji Sanatan

Har’ila Yau Sanatan Yace a taron an bayarda Gudummawa masu mahimmanci da hangen nesa da tasiri sosai Dukkanin mahalarta sun amince da Kira tare da gaggauta zartar da Dokar.

Manufar Dokar gyaran tsarin Makamai (Gyara), 2021 na neman sanya hukunci mai tsauri kan laifuka a cikin tsarin Dokar da kuma tanadin lalata bindigogin da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba cikin kasar ko kuma mallakar mutane ba tare da ingantattun lasisi ba. Babban makasudin yin kwaskwarimar shi ne takaita yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma samar da dokar da ta dace da kyawawan halaye na duniya. Gyaran zai kuma magance wasu matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya a halin yanzu. Inji Sanata uba sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *