Labarai

Majalisar dattijan Nageriya ta samu cigaba Mai Tarin yawa Sakamakon jagorancin Sanata Ahmad lawan ~Sanata Uba sani

Spread the love

A wani Sakon Taya murna Daya wallafa a shafin sa na Facebook Sanata Uba sani Kuma Dan takarar Neman Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar Apc yana cewa na kasance tare da manyan takwarorina, masoya dimokuradiyya da kuma masu fatan alheri a Najeriya da ma duniya baki daya wajen taya jagoranmu, haziki kuma mai hazaka shugaban sanatoci Kuma Shugaban majalisar dattijai ta tara, Sanata (Dr) Ahmad Lawan, GCON. yayin da yake cika shekaru 64 a duniya. Karkashin jagorancin ku mai tasiri, hada kai da kuma samun sakamako, Majalisar Dattawa da Majalisar Dokoki ta kasa sun samu kwanciyar hankali da ci gaba mara misaltuwa.

Ya kasance babban farin ciki da girmamawa aiki tare da ku. Masu neman shugabanni da kuma waɗanda ke kan madafun iko a halin yanzu suna da abubuwa da yawa da za su koya daga tsarin gina yarjejeniya.

 Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ci gaba da yi wa jagoranmu jagora da karfafa gwiwa a yayin da ya sake sadaukar da kansa wajen yi wa Nijeriya hidima da bil’adama.

Sanata Uba sani shine Dan takarar gwamnan a jihar Kaduna Mafi karfi da samun karbuwa a duk cikin ‘Yan takarkarun sauran jam’iyyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button