Labarai

Majalisar wakilai ta dakatar da yin gwanjon kadarori 11 na Kamfanin hako mai na kimanin $1bn

Spread the love

Majalisar Wakilai a ranar Larabar da ta gabata ta bukaci Kamfanin Raya Man Fetur (NPDC) da ya dakatar da shirin yin gwanjon kadarori 11 na Kamfanin hako Mai na OML.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na muhimmancin kasa da Hon. Victor Mela a zauren majalisa a Abuja.

A nasa jawabin, Mela ya ce rijiyar mai da ke karkashin OML 11 a da ta kasance karkashin hadin gwiwa ne na kamfanin Shell Petroleum Development Company (SPDC).

Ya ce filin ya kasance babu aiki tun lokacin da aka fatattaki kamfanin daga yankin Ogoni a shekarar 1993.

Dan majalisar ya bayyana cewa kotun daukaka kara a ranar 16 ga watan Agustan 2021, ta yanke hukuncin cewa hadaddiyar kungiyar SPDC ta rasa hakkinta na sabunta lasisin aiki.

Ya jaddada cewa akwai matsalolin da ba a warware ba tsakanin gwamnati da al’ummomin Ogoni.

Mela ya nuna damuwarsa kan ikirarin cewa gwamnati na da hannu a shirin yin gwanjon kadarorin OML 11 ga kamfanin Sahara Energy Limited a kan dala miliyan 250 sabanin dala biliyan 1 da SPDC ta bayar.

Don haka majalisar ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin man fetur (Upstream) da ya binciki shirin gwanjon da sauran batutuwa, tare da bayar da rahoto a cikin makonni hudu don ci gaba da aiwatar da dokar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button