Labarai

Malami ya ce mutane ba su da dalilin da zai sa ba za su zabi jam’iyar APC ba a kowanne mataki ~Cewar ministan shari’a Malami SAN

Spread the love

Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na yankin Kebbi ta Kudu da aka gudanar a garin Yauri da ke karamar hukumar Yauri.

Ministan ya ce: “Kafin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, Najeriya tana kashe Naira tiriliyan 1.5 wajen shigo da shinkafa daga kasar Thailand da sauran kasashe a duk shekara, amma juyin juya halin shinkafa da shugaban kasar ya bullo da shi ya kawo karshen hakan.

“A yau, ina mai farin cikin sanar da ku cewa Najeriya ba ta shigo da shinkafa daga waje, maimakon haka, muna fitar da shinkafa sama da tan 800 a duk shekara, ba shakka, wannan babbar nasara ce.”

Malami ya ce mutanen Kebbi ba su da dalilin da zai sa ba za su zabi APC a kowane mataki, yayin da ya ba da misali da nadin da gwamnatin tarayya ta yi wa ‘yan asalin jihar Kebbi da suka hada da; Babban Darakta na Kogin Sokoto, Manajan Darakta, HYPPADEC, Shugaban Hukumar EFCC da Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), da dai sauransu.

Ya lissafa ayyukan da gwamnatin APC ta aiwatar a jihar da suka hada da; gina titinan Sokoto zuwa Kontagora, shirin anchor borrower’s program, tsarin jin dadin jama’a, karfafa matasa da kudaden tsira da sauransu.

Ministan ya yi kira ga al’ummar Kebbi da su zabi jam’iyyar APC, inda ya bukaci “su amince da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar a kowane mataki domin su ci moriyar dimokradiyya a yankunansu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button