Masarautar jihar Katsina ta tsige hakimin Ƙanƙara

Masarautar Katsina Ta Sami Hakimin Kankara Da Hannu Wajen Taimakawa ‘Yan Bindiga, Ta Tsige Rawaninsa Gaba Daya

Labarin da muke samu daga Katsina Daily Post News na cewa, Majalissar Sarkin Katsina ta sami Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara Alh Yusuf Lawal, da hannu wajen taimakawa yan bindiga, a don haka ta kore shi kwatakwata daga kujerar da yake bisa kai ta sarauta a masarautar.

Za a iya tuna cewa a kwanakin baya ne masarautar Katsina ta dakatar da Hakimin sakamakon zarginsa da taimaka wa yan bindiga masu kai hare-hare a jihar.

Sakataren fadar masarautar Katsina, kuma Sarkin Yakin Katsina Alh Bello Mamman Ifo shi ne ya tabbatar da labarin hakan ga majiyarmu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *