Fiye da makonni uku bayan an sace sarkin garin Ikuru a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas, Aaron Ikuru, daga fadarsa, wadanda suka sace shi suna neman kudin fansa N5bn don ya shaki iskar ‘yanci.
Kakakin fadar, Maurice Ikuru, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce masu garkuwar sun yi wannan bukatar ne lokacin da suka tuntubi danginsa.
“Sun ce suna son N5bn. Amma ban sake jin komai daga gare su ba. Amma mun dogara ga Allah cewa nan ba da dadewa ba, za a sake shi, ”in ji Maurice.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, Nnamdi Omoni, ya bayyana fatan cewa nan ba da dadewa ba za a saki sarkin.
Ya ce sakin wani malami na Jami’ar Fatakwal, Dokta Jones Ayouwo, a ranar Litinin, zai share fagen sakin sarkin, yana mai cewa a yanzu ‘yan sanda za su haskaka fitilar bincikensu ta wannan hanyar.
Omoni ya bayyana cewa, “Sakin malamin na Jami’ar Fatakwal ya share fagen sakin sarki nan ba da jimawa ba.
“Ba ma hutawa. Sashinmu na Yaki da Satar Mutane da duk wasu dabarun aiki suna aiki ba dare ba rana. Lamari ne na tsaro, don haka ba za mu bayyana komai ba.
“Ba ma son yin amfani da karfi na makamai, amma muna aiki tukuru don tabbatar da cewa ya fito lafiya ba tare da rauni ba.”