Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe wani Basarake.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kashe Oba Adegoke Adeusi, Olufon na Ifon a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

An kashe Oba Adeusi a yammacin Yau Alhamis a wani wuri kusa da yankin Elegbeka na garin.

Sarkin yana dawowa daga fadarsa daga Akure, babban birnin jihar, lokacin da aka kashe shi.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa tun da farko an sace Oba Adeusi kafin a kashe shi.

Majiyar ta ce, “tun da farko sarkin ya halarci taron tare da dukkan Obas a Akure kuma yayin da yake kan hanyarsa ne aka sace shi wanda ya haifar da fargaba a cikin al’ummar.

“Amma yayin da muke kokarin tabbatar da kubutar da shi, sai muka ga ashe tuni masu garkuwar sun kashe shi. Abin bakin ciki ne matuka.”

Wasu na ganin Satar mutanen ko dai so yake ya mamaye Kasar sabanin Yadda aka San Abin yafi faruwa a Arewacin Kasar Ne.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.