Labarai

Mata da matasan jam’iyar APC sunsha Alwashin bayarda kuri’u Milyan arba’in 40m ga Bola Tinubu a zaben 2023 Mai zuwa.

Spread the love

A Yau ranar Alhamis ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa mata da matasa a Najeriya za su baiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa, Alhaji Kashim Shettima kuri’u miliyan 40 a zaben 2023 mai zuwa.

Da take jawabi a taron yakin neman zaben a Ilorin, shugabar mata ta jam’iyyar ta kasa, Binta Edu, ta bukaci matan da su yi watsi da duk wani abu da ke damun su, inda ta kara da cewa, “yarjejeniyar ita ce zamu bayarda kuri’u miliyan 40 ga ‘yan biyu na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. da Kashim Shettima.

“Muna da babban dan takara a Sanata Tinubu da kuma abokin takararsa. Su biyun ne za su kai Nijeriya kasar da ta ke mafarki na gaba Wannan shi ne lokacin da za a hada kai,” in ji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button