Matar Gwamna Masari ta raba kayan abinci ga matan yankin Daura. 

Matar Gwamnan Jahar Katsina, Hajiya Zakiyya Aminu Bello Masari ta raba kayan abinci ga wasu mata a kananan hukumomi guda bakwai a yankin Daura.

Wananan rabon kaya ya auku ne a sakatariya ta hakaramar hukumar Mani kuma kayan za a rabawa mata ne a kananan hukumomin da suka kunshi Mani, Mashi, Kusada, Bindawa, Ingawa, da Kankia.

Tace wannan rarraba na daya daga cikin tallafi ga al’umma wanda ta bayar zuwa ga mata a cikin watan Ramadan.

Ta kuma kara da cewa, kungiyar NGO dinta (Kungiya mai zaman kanta) mai suna Women Youth and children improvement support zai hada da shirye shiryen hanyoyi wanda za a tallafawa mata da matasa a yankin Daura.

Durbin Katsina, hakimin Mani, Alhaji Umar Babani Mani ya nuna yabawa ga matar gwamna a kan damuwar ta da yanayin da masu karamin karfi suke ciki.
Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *