Mazauna Gari sunyi Jarumta sun kashe ‘yan ta’adda mutun talatin 30 a jihar Katsina.

Rahotanni daga jihar katsina na Cewa Akalla ‘Yan Bindiga mutun 30 mazauna yankin da kuma’ yan banga na kauyen Majifa da ke karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina Suka kashe.

Kodayake bayanan da ke tattare da lamarin ba su da yawa a lokacin rubuta wannan rahoton, majiyarmu ta gano cewa mazauna kauyen sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna.

Wani mazaunin garin ya shaida wa majiyarmu cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin din. a kalla 30 daga cikin ‘yan fashin, sun mutu” in ji shi.

Amma, ya kara da cewa sauran maharan sun ruga Kan ababan Hawa don kwaso gawarwakin, yana cewa, “Yayin da mazauna kauyen ke jiran hutun rana don kone gawarwakin, sai suka farka ganin sun kwashe gawawwakin, tare Sauran kauyukan da ke tabbatar da cewa wasu mutane sun yi hakan ta hanyar amfani da rakuma. ”

Wannan shi ne karo na uku a cikin makonni uku da mazaunan suka tunkari ’yan bindiga.

A ranar Lahadin da ta gabata, mazauna garin Magama da ke cikin Karamar Hukumar Jibia sun tunkari maharan inda suka kashe uku daga cikinsu.

Hakazalika, mazauna kauyukan Yan Marafa da Mununu a karamar hukumar Faskari da ke cikin garin Katsina sun jajirce wa maharan yayin da aka kashe adadi mai yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *