Milyan dari Biyu 200m masarautar Kano ta karba na rashawa Kan filaye ~Inji Muhayi Magaji

Shugaban Hukumar koke-koke da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya zargi Shugabannin majalisar masarautar ta Kano, karkashin Alh. Aminu Ado Bayero, da karbar kudi har naira miliyan 200 a badakalar siyar da filayen Gandun Sarki a rukunin gidajen Dorayi.

A cewar Muhuyi, mai martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Bayero da mukarrabansa na fuskantar tuhuma daga hukumarsa kan shigarsu sayar da kadada 22 mallakin masarautar Kano.

Muhuyi ya lura da cewa, duk da cewa sarki Bayero ya musanta masaniya kan yarjejeniyar mallakar filayen da ake shakku a kai, amma bincike ya nuna cewa a kalla makusantansa uku suna da hannu dumu-dumu a cikin lamarin.

Yayin da yake bayanin yadda hukumarsa ta gano wannan cinikin, Muhuyi ya ambaci wani mutum da ake kira Yusuf a matsayin wanda ya sayi kadada 14 daga Masarautar kan kudi Naira miliyan 200.

Shi (Yusuf) ya sanya hannu kan wata yarjejeniya cewa ya sayi kadada 14 a kan kudi Naira miliyan 200. Ya ba su tsabar kudi Naira miliyan 200 kuma Majalisar Masarautar ta yi alkawarin ba shi lambar asusun wanda zai sanya wani Naira miliyan 200, ”in ji Muhuyi.

Wani makusancin Sarki Aminu Bayero, Sarki Waziri, wanda shi ne Dan Rimin Kano kuma Mataimakin Sakataren Masarautar, a wata yarjejeniya da hukumar ta gani, ya rubuta cewa ya sayar da filayen ne a madadin Majalisar Masarautar.

Duk da haka, hukumar ta gano cewa Awaisu Abbas Sanusi, wanda babban jami’i ne a ofishin Sakataren Masarautar, shi ne wanda ya karbi tsabar kudi Naira miliyan 200, amma, ‘yan kwanaki bayan haka ya musanta cewa yana da wani kaso a cikin wannan kasuwancin.

“N200 miliyan shine adadin cin hancin da aka karba, sannan kuma sai wata Naira miliyan 200 da za a sanya a cikin asusun Emirate shi ne kudin da za a rubuta a hukumance,” in ji Muhuyi.

“Me yasa Masarautar za ta amshi tsabar kudi dala 416,000? Me majalisar ke amfani da wannan makudan kudaden, duk da cewa tana da asusun ajiya, ciki har da na dala ?, ”in ji shugaban yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kuma lura cewa hatta Naira miliyan 200 da ke takaddama ba a sanya su a cikin wani asusun bankin Masarautar ba, bayan da Awaisu ya tara kudin.

Muhuyi ya jaddada cewa an sayar da filayen ba tare da kimantawa ba, wanda shima laifi ne a karan kansa. “Ba za ku iya sayar da filayen gwamnati ba tare da kimantawa ba.”

Don haka, Muhuyi ya yi alfahari cewa ba zai bar mai siyan filin ba, don haka zai tabbatar da an tuhume shi da laifin hada baki.

Muhuyi ya kuma jaddada cewa hatta Gwamnan jihar Kano ba zai iya hana shi gudanar da wannan binciken ba.

Sahelian times

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *