Mun kusa Kara Farashin litar man fetir ~Buhari.

Gwamnatin tarayya ta ƙara jaddada wa yan Najeriya cewa su shiryawa ƙarin farashin man fetur saboda matsin tattalin arziƙin da ƙasar ke ciki.


Karamin ministan mai, Chief Timipre Sylva, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wajen yaye ɗalibai da basu kyaututtuka a jami’ar Patakwal, jihar Rivers. Sylva yace nan bada jimawa ba gwamnati zata zare tallafin man fetur, wanda a cewarsa wasu yan kasuwa ne kaɗai ke amfanaa da tallafin, kamar yadda Punch ta ruwaito.


Ministan yace: “Abun takaici ne idan aka sami ƙarin farashin litar mai, to nan danan zai karaɗe kasuwa kuma bamujin dadin hakan. Musamman shugaban ƙasa baya son cire tallafin amma matsin tattalin arziƙi ya mana illa sosai.” “Shin zamu cigaba da bada tallafin man fetur, wanda talaka baya amfana dashi, amma wasu ɗai-ɗaikun yan kasuwan ƙasar nan kaɗai ke amfana dashi? Bana son in bayyana mutanen dake amfana da tallafin.”


Yan Najeriya basa amfana da tallafin mai kai tsaye, babban abinda keda alaƙa da yan Najeriya shine kalanzir da mutanen karkara ke amfani dashi wajen girki, sai kuma man fetur da suke mfani dashi wajen tafiye-tafiye. Dukkan waɗannan ba’a ƙayyade farashin su ba na tsawon lokaci.” Sylva ya ƙara da cewa gwamnati zata cigaba da biyan tallafin mai na wani lokaci saboda yanzun ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki ne a kan lamarin. Yace da zarar an kammala tattaunawa da masu ruwa da tsakin, za’a sanar da zare tallafin kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *