Labarai

Muna Alfahari da gwamna Yahaya Bello a kan batun harkokin tsaro a jiharsa ta Kogi ~Cewar Shugaba Buhari.

Spread the love

Shugaban, wanda ya kai ziyarar aiki domin Bude wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar, ya lura cewa gwamnan ya yi matukar kokari a fannin tsaro da aiwatar da ayyuka.

Ya ce musamman gwamnatin tarayya tana alfahari da Gwamna Bello, wanda ya ce ya nuna tabbacin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi fice a Najeriya.

“Na gamsu da yadda Gwamna Yahaya Bello ya yi kokari matuka a fannin tsaro da aiwatar da ayyuka a jihar Kogi. Muna alfahari da shi kuma muna rokonsa da ya kara yi wa jama’a. Ina kira ga al’ummar jihar Kogi da su ba shi goyon baya, domin ya samu nasara da kuma samar da ribar dimokuradiyya.”

Shugaban, wanda ya yi matukar farin ciki da ganin irin abubuwan ban sha’awa a lokacin ziyarar tasa, a asibitin Reference, Okene, ya sake taya gwamnan murna

Ya kara da cewa yahaya da tawagarsa sun bani karin haske game da dimbin ayyukan da za mu so a yi muku a fadin jihar, ciki har da sabuwar jami’ar Confluence University of Science and Technology, CUSTECH, da ke Osara, da Confluence Rice Mills. a Ejiba, da hanyoyin sadarwa na gari daban-daban a Idah, Okene da Kabba da kuma hanyoyin cikin jihar a shiyyar sanatoci uku da babban aikin zaizayar kasa a Ankpa, Ogugu da sauran wurare, da sauran hanyoyi, asibitoci, makarantu da sauran muhimman ababen more rayuwa Inji Shugaba Buhari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button