Muna Bukatar Sanin Gaskiya Akan Lafiyar Buhari – Oby Ezekwesili

Tsohuwar ministar Najeriya, Oby Ezekwesili, na kira ga kungiyar Likitoci kan Shugaba Buhari. Ezekwesili ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter:

Ina tsammanin cewa a wannan matakin da muke ciki na rauni ya kamata mu san lafiyar shugaba buhari domin muna cikin ruɗu ta yadda yayi shiru da abin da muke ciki na ƙunci da rashin tsaro a Tarayya da sauran Jahohi Alhali muna da ‘yancin sanin hakan a dokance.

Lallai ya zama dole mu tantance kuma mu sani cewa shugaban kasa na iya gudanar da ayyukan ofis Kuwa?

Dan haka muke kira ga ‘Yan ƙasa da su matsa gaba ɗayan mu domin ganin cewa ko da kwamiti za a yi lallai muna Son sanin a wana hali Shugaba Muhammadu Buhari ke ciki.

A matsayina na ‘yar kasa mai matukar damuwa, don haka ina neman #MedicalPanelOnBuhari tunda ba za mu iya amincewa da Likitan Gidan Gwamnatin ya ba mu cikakken bayani ba.

Abinda muke bukata yanzu shine waɗanda abin ya shafa su fito su yi mana cikakken bayani game da lafiyar Buhari.

Ya kuke kallon wannan Buƙata?

Leave a Reply

Your email address will not be published.