Mutane biyun da aka gani sun diro daga jirgin su Marigayi Janar Attahiru Direbobin jirgin ne – Majiya.

Wata majiya ta bayyana mana vewa Mutum biyun da shaidun gani da ido suka gansu sun diro daga cikin Jirgin da su Janar Attahiru sukai hadari kafin ya fado kasa matukan Jirgin ne,(Pilots).

Idan baku manta ba wasu shaidun gani da ido wadanda suke kusa da wajen da jirgin yayi hadari sun ce sun ga mutane biyu sun diro daga jirgin yayin da jirgin yayi hadarin.

Ganin dirowar mutanen ta sa al’umma da dama sunata tofa albarkacin bakinsu, kowa yana ta yin hasashe daidai da ra’ayinsa.

Majiyar ta ce lokacin da matukan Jirgin suka gano cewa jirgin ya sami matsala ne sai suka zari laimar tashi suka fito daga cikin jirgin suka dira zuwa kasa.

Daga Kabiru Ado Muhd

One thought on “Mutane biyun da aka gani sun diro daga jirgin su Marigayi Janar Attahiru Direbobin jirgin ne – Majiya.

  • May 25, 2021 at 12:45 pm
    Permalink

    Wallahi karyane kuma Allah yaisa bamu yafeba suncecemu su waanda sukayi hakan sunsan kansu kuma Allah yasansu Allah yaisa Allah yaisa Allah yaisa

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *