Mutum 18 sun mutu yayin da Kwale-kwale ya kife a Bauchi.

Akalla mutane 18 ne suka mutu a lokacin da kwale-kwalen da ke dauke da manoma 23 ya kife a jihar Bauchi.

Duk da cewa an ceto mutane biyar da ransu, amma direban da fasinja daya ba su cikin hayyacinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a Bauchi.

A cewarsa, mamatan sun hada da yara takwas, matasa takwas, da kuma manya biyu.

Ya ce lamarin ya faru ne a Kogin Buji da ke karamar hukumar Itas Gadau a jihar Bauchi. Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published.