N2,500 muke Sai da buhun siminti a Nageriya wanda shine mafi Arha a nahiyar Africa ~Inji Akiko Dangote

Kamfanin Dangote yace farashin da yake sayar da Sumunti a Najeriya shine mafi Arha a Africa.

Kamfanin ya bayyana cewa a reshensa dake Obajana da Gboko, yana sayar da Simunti akan Naira 2,450. Sai kuma Simintin Reshensa dake Ibese yana sayar dashi akan Naira 2, 510 hadda kudin harajin VAT, Watau Farashin kamfani.

Wannan bayani na zuwane yayin da Rahotanni suka nuna cewa, Kamfanin na Dangote na sayar da Sumunti akan farashi mafi tsada a Najeriya fiye da wasu kasashen Duniya, irinsu Ghana da Zambia.

Daya daga cikin Shuwagabannin kamfanin, Devakumar Edwin ne ya bayyana haka ga manema labarai.

0 thoughts on “N2,500 muke Sai da buhun siminti a Nageriya wanda shine mafi Arha a nahiyar Africa ~Inji Akiko Dangote

 • April 13, 2021 at 9:25 am
  Permalink

  A gaskiya mutanen Nigeria ba sa ga wannan saukin

  Reply
 • April 13, 2021 at 12:52 pm
  Permalink

  To ranka ya dade mu dai Nan a Zaria 3800 ne meke faruwa me?

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *