Na Allah basa karewa a Duniya: Wani mai yin haya a mashin ya tsinci Miliyan 10 ya nemi mai kudin ya mayar masa da abun shi, an bashi kyautar dubu 500,000 yaki amsa yace Allah ya keso ya biya shi

Ayaune na samu labarin wannan Bawan Allah mai suna Sale wanda akafi sani da ( wuta sale ) wanda ke zaune a Garin Kankia lg katsina state . Tabbas samun irin wannan Bawan Allah achikin Al’umma abin Ayabane Domin kuwa yayi abin Ayaba Masa sosai . Domin kuwa ba Dukkanin mutane bane zasuyi abinda wannan matashi yayi .

Yarone matashi mai sana’ar Express kuma Yana daya Daga chikin Yan Agajin na Jami’atu izatul Bidia wa’ikamatus sunnah reshen karamar Hukumar kankia katsina state .

Wannan Abu ya farune a chikin Karamar Hukumar kankia dake a jahar katsina , Yayi kokari matuka Domin kuwa sai wanda Allah keso da Rahamarsa har zai tsinci irin wadannan makudan kudi yakuma bada. Ina roka Masa Allah ya kara kama Masa Adukkanin lamurransa Allah kuma ya kara tsarkake zukatanmu ameeen.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *