Na Bawa Isra’ila Wa’adin Sa’a 24 Ta Daina Kashe Fararen Hula, ~ Inji Kim Jong’un

Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa, mr kim jong’un ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da hare haren da Isra’ila ke kai wa a kan fararen hula a zirin Gaza.

Mr Kim, ya ce kamata yayi ace an zauna a kan teburin sulhu domin warware wannan rikici mai makon amfani da ƙarfin soji, kuma ya kamata ace ƙasashen duniya sun takawa Isra’ila burki amma tunda sun kasa mu ba zamu bari wannan zaluncin yaci gaba ba.

Saboda haka.mun bawa Isra’ila wa’adun sa’a 24 ta dakatar da kai gare hare a kan fararen hula ko kuma ta ɗan ɗana kuɗarta, domin kuwa a shirye muke da mu bada ko wace irin gudun mawa domin taimakawa fararen hula in ji Kim Jong’un, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ba ƙasar ya bayyana.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *