Labarai

Na matsu na Gama mulki na koma gida Garin Daura ~Cewar Shugaba Buhari

Spread the love

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a ranar Talata, ya ce yana fata Kuma ya matsu ya komawa garin Daura nan da watanni biyar masu zuwa, a karshen wa’adinsa.

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) a fadar gwamnati da ke Abuja.

Buhari wanda ya godewa ‘ya’yan kungiyar bisa gaggarumin addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa da kuma kasa, ya yabawa kungiyar Musulunci kan yadda ake ci gaba da yin hakuri da addini a kasar.

Sanarwar mai suna ‘Shugaba Buhari ya yabawa kungiyar Islama kan yadda suke karfafa hadin kan addini.

Shehu ya ci gaba da cewa, “Shugaba Buhari wanda ya godewa ‘ya’yan kungiyar bisa gaggarumin addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa da kuma kasa, ya ce yana fatan komawa garin Daura nan da watanni biyar masu zuwa a karshen wa’adinsa.

Shugaban ya shaidawa kungiyar a karkashin jagorancin Khalifan Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya), Sheikh Muhammad Khalifa Niass, cewa ya yaba da rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afirka da dama.

A yayin ziyarar ban girma da kungiyar ta kai Sheikh Tijjani Shehul Hadi Almauritany ya gabatar da addu’o’i ga shugaban kasa da kasa da kuma ‘yan Najeriya yayin da Sheikh Abdullahi Lamine ya gudanar da karatun kur’ani mai tsarki.

A nasa jawabin, Khalifan kungiyar, Sheikh Niass, ya ja hankali kan tarihin Manzon Allah SAW, da irin darussan da musulmi za su iya yi daga tsarin rayuwarsa.

Da yake jaddada wajibcin tuba na gaske, kamar yadda koyarwar kur’ani mai tsarki ta bayyana, Sheikh Niass ya yi alkawarin cewa kungiyar Attijaniyya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai, kamar yadda koyarwar Littafi Mai Tsarki da Musulunci suka tanada.

Khalifah Niass ya kuma ba da labarin irin kusancin da mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Niass ya yi da Nijeriya da al’ummarta, wanda ya kai shekaru saba’in, inda ya ce iyalin sun kuduri aniyar ci gaba da kulla alaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button