Labarai

Na roki al’ummar jihar Kaduna da su zabi Bola Tinubu a zaben na 2023 ~Cewar Uba sani.

Spread the love

Sanata Uba sani ne ya bayyana hakan a taron Kaduna KADIVEST Yana Mai cewa A yau na kasance na hadu da Mai Girma Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i da Mataimakiyar Gwamna H.E Dr. Hadiza Balarabe da ‘dan takarar Shugaban kasa na jam’iyar APC Asiwaju Bola Tinubu da Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aliko Dangote da sauran manyan baki a bukin Kaduna karo na bakwai. Taron Tattalin Arziki da Zuba Jari (KADINVEST 7.0).

Ina taya maigidana kuma shugabana, Gwamna Nasir El-Rufai da jiga-jigan tawagarsa murnar ci gaba da KADINVEST tare da daukaka ta zuwa babban taron bunkasa kasuwanci a Najeriya. Jihar Kaduna dai an dora ta a kan tabbatacciyar hanya ta tabbatar da abubuwan da ya dace.

Na yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna nagari da masu zuba jari da kuma abokan zamanmu na ci gaban kasa cewa gadon Mallam Nasir El Rufa’i ba Abu bane Mai sauki Amma a shekaru masu zuwa za a ci gaba da da biyan bukatunmu na gamayya.

Na kuma bi Gwamna Nasir El-Rufai a yayin da ya jagoranci tawagar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen yi wa mahaifinmu mai martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bamalli gaisuwar ban Girma a fadarsa dake Zaria. A lokacin da nake mika kuri’ar godiya a wajen taron, na bukaci al’ummar jihar Kaduna da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin marawa dan takararmu na shugaban kasa da jam’iyyar APC kuri’a a babban zabe mai zuwa.

Kaduna na cigaba da samun cugaban harkokin more rayuwa fiye da ko wacce jiha a Nageriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button