Na warware fatawowina da ke da kuskure a baya – Pantami

Ministan Sadarwar Nijeriya Dr Isah Ali Pantami ya ce ba ya goyon bayan ta’addanci. A cikin Tafsirin Ramadan na wannan Asabar da ya gudanar a masallacin Annur da ke Abuja wanda DCL HAUSA ta bibiya ya ce fatawarsa da ya bayar shekaru 20 da suka wuce ba dole ba ne ta zama fahimtarsa ta yanzu ba.

Pantami ya ce a cikin shekarun da ya yi yana da’awa ya sauya fatawa sama da 100 bayan da ya gano akwai kura-kurai a cikinsu. Wasu masu zargin malamin sun nuna wasu daga cikin fatawowinsa a baya cewa ya nuna goyon baya ga Osama Bil Ladan tare da yin wasu lakcoci da ke tunzura rikici. Malamin ya ce fatawowinsa na baya-bayan nan sun canza da na baya domin a yanzu ya sake gogewa da wayewa a harkar da’awa.

Dr Isah Ali Pantami ya ce siyasa ce ta sa wasu a yanzu suka fito da wasu bayanai inda suke son bata masa suna, yana mai jaddada cewa shi baya goyon bayan a yi yaki kowane iri. Ya ce, “ka taba ji na sanya wa dana sunan wani da ake ganin dan ta’adda ne?”

Rahoto- Ahmad Aminu Kado..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *