Najeriya Na Bukatar Ire-iren Pantami A Mulki, Za Kuyi nadama Idan Ya Bar mukamin sa na mulki~ Gumi Yayi Gargadi

Wani malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa ‘yan Nijeriya za su yi nadama idan aka tsige Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Ali Pantami daga mukamin sa.

‘Yan Najeriya na ci gaba da matsa lamba kan fadar shugaban kasa kan ta kori ministan yayin da wasu ke ta kiraye-kirayen ya yi murabus saboda wasu bayanai da ya yi na nuna goyon baya ga kungiyoyin’ yan ta’adda a baya.

Amma Gumi, wani mai wa’azin addinin Islama da ke zaune a Kaduna wanda ke yawan kira ga tattaunawa da ‘yan fashi ya bayyana cewa Pantami ba ya tare da yan ta’adda

Gumi, wanda yayi magana a wata hira da gidan talabijin na Roots TV ya ce Ministan da ke cikin rudanin ya kasance mai gina kasa ne wanda ke kokarin jawo hankalin sauran matasa na don marawa gwamnati baya.

Ya ce “Nuna mini mutum daya da ya kashe.  Bai kashe kowa ba.  Bai ba da umarnin a kashe kowa ba.  Mutumin yana kokarin daidaita gwamnati a tsakanin wani bangare na matasa wanda muke so su zo su shiga aikin gina kasa. ”

Gumi ya kuma ce Pantami ya sha fama da muggan kamfe na tsige shi daga mukamin sa. “Kuma ku mutane kuna kokarin yaki da shi.  A’a ya kamata a kara samun mutane kamar Pantami a basu mulki.  Kar a cire shi.  Za ku yi nadama” kashedin sa kenan.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *