Nan da shekarar 2021 yawan bashin da ake bin Najeriya zai karu da tiriliyan 7.67, Cewar Gwamnatin Tarayya.

Ministar kudi da tsara tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa nan da watan Disamba na shekarar 2021 bashin Najeriya zai karu zuwa Naira Tiriliyan 38.68.

Ta bayyana hakane a yayin da ta gabata a majalisa wajan Kwamitin dake kula da basukan cikin gida dana kasashen waje.

Ofishin gwamnatin tarayya dake kula da ciwo bashi ya bayyana cewa a watan Yuni da ya gabata, ana bin Najeriya bashin Tiriliyan 31.009.

Jaridar The cable ta ruwaito Zainab Shamsuna Ahmad na cewa nan da shekarar yanzu bashin dake kan Najeriya jihohi da gwamnatin tarayya Tiriliyan 31.01 ne kuma nan da watan Disamba zai karu zuwa Tiriliyan 32.51 hakanan nan da watan Disamba na shekarar 2021 zai kuma karuwa da Tiriliyan 38.68.

Zainab ta bada shawarar cewa ya kamata gwamnati ta rika daukar wasu ayyuka kalilan tana maida hankali kansu a gamasu kamin a kama wasu.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published.