Labarai

Nazo Adamawa ne domin na tabbatar da mace ta farko amatsayin gwamna a Nageriya ~Cewar Shugaba Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasancewarsa a taron yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, APC shine don tabbatar da zaben ‘yar takarar gwamna, Sen. Aisha Dairu Ahmed Binani a matsayin mace ta farko da aka zaba gwamna a kasar.

A safiyar yau, Litinin, Buhari ya yi wa jam’iyyar APC yakin neman zabe tare da mika tutocin jam’iyyar ga dimbin magoya bayansa a fadar Lamidon Adamawa da ke Yola, jihar Adamawa.

Shugaban ya kuma gabatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, da ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa ta APC, Binani ga magoya bayan jam’iyyar.

Shugaban ya ce zaben da aka yi wa Binani a matsayin Yar takarar Gwamnan Adamawa zai bude wa mata a kasar dama kuma ya aike da sako ga duniya game da Adalcin shugabancin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button