Ni na fara kawo dabarar zantawa da yan ta’adda, kuma Buhari yayi hakuri da cin kashin da mutane ke masa ~inji Masari 

Sabanin abinda wasu ke cewa, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya fada cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai gaza wa yan Nijeriya ba.
Massri yayi magana a intabiyu ta Television Continental wadda akayi a Abuja a ranar lahadi a inda yace yakamata yan Nijeriya su yabi Buhari akan yin hakuri da cin kashin da mutane ke mai.

Ya fada cewa “muhimmancin shugaban kasa bai canja ba, duk wanda yace darajar Buhari tayi kasa to ya jira har sai lokacin da za a sake yin wani zabe.

“Dole ne a samu rashin amincewa da wasu abubuwa a mulkin demokaradiyya, a inda ma ake gudanar da mulkin demokradiyya mafi kyau zaka samu wasu mutane basu amince da wasu abubuwa ba. Ba za’a ce mutane bazasu ki nuna rashin amincewar su ko suyi zanga zanga akan abinda bai masu ba saboda demokradiyya ake ba.

“Ban tunanin cewa Buhari ya gaza, hasalima, a tunani na ya yi hakuri da mu. Mun taba yin wani shugaban kasa wanda bai dauki cin kashin da Buhari ya ke dauka daga wasu mutane ba”
Ya kwatanta jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya mafi karfi, amintatta da kuma abin dogaro akai.
Masari ya dada da cewa abinda ya ja rushewar tattaunawar da akayi tsakanin gwamnatin sa da yan shine rashin tsari na shugabanci a tsakanin yan ta’addan.

Yace “Ni na fara kawo dabarar zantawa da yan’ ta’adda tun a shekarar 2016 tare da hadin gwiwar shuwagabannin jami’an tsaro muka kai ziyara a inda yan ta’addar suke zama.

“Wasu daga cikinsu sun ajiye takoban su amma daga bisani al’amarin ya ci gaba a inda aka sace daliban Kankara

“Ba’a samu nasara a waccan tattaunawar bane saboda rashin tsari na shugabanci a tsakanin yan ta’addar. Sun rarrabu ne a gungu daban daban da rukuni kala kala” A cewar sa.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *