Labarai

Obasanjo ya gargadi ‘yan Nageriya kan cewa karsu kuskura su zabi Atiku Saraki Tambuwal da Peter Obi.

Spread the love

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi ‘yan Najeriya kan kada su zabi wasu ‘yan takarar shugaban kasa wanda suke ikirarin cewa wasu kungiyoyin siyasa ko matasa ne suka siya musu fom din tsayawa takara.

Obasanjo ya yi wannan tsokaci ne a Legas yayin wani taro na bikin cika shekaru 61 na Fasto Itua Ighodalo.

An sayi fom din takarar shugaban kasa ga wasu ‘yan takarar Neman shugaban kasa na jam’iyyar PDP a makonnin baya da suka hada da tsohon mataimakin Obasanjo, Atiku Abubakar, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki. Sauran sun hada da gwamnan jihar Sokoto; Aminu Waziri Tambuwal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Amyim, da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

A ranar da Obasanjo ya yi wannan tsokaci, ‘yan gidan fitacciyar shirin Brekete a gidan rediyon kare hakkin bil’adama na Abuja sun saya wa Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom fom din tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button