Ofishin manajin basussuka Ya Bayyana Cewa Bashin da ake Bin Najeriya yakai N33.63 Trillion.

Patience Oniha, Dirakta Janar ce a Ofishin manajin basussukan Najeriya DMO, , ta Bayyana cewa basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yanzu ya kai Kimanin N33.63 trillion.

A wani Jawabi data wallafa a Shafinta Na Twitter Patience Oniha tace jita-jitar da ake Yaɗawa kan adadin bashin da ake bin ƙasar ne yasa ta wallafa jerin basussuka Domin Kowa Ya gani.

Ta ƙara da Cewa “yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne da birnin tarayya, da Kuma jihohin Najeriya 36,”

“A bangaren gwamnatin tarayya, adadin bashin da aka karɓa ya ƙaru ne saboda faɗuwar farashin ɗanyen mai a 2015.”

“Amma a kasafin kuɗin 2018 zuwa 2020, adadin basussukan sun ragu.”

“Abin takaici, illar annobar COVID-19 kan kuɗin shiga ya sabbaba tashin basussukan.”

Idan Za ku tuna cewa a karshen shekarar 2020, DMO ta ce bashin da ake bin Najeriya ya kai N32.9tr.

Ahmad Aminu Kado….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *