Pakistan za ta kori jakadan Faransa kan ba da ƴancin yin ɓatanci ga Annabi

Pakistan za ta kori jakadan Faransa
Gwamnatin Pakistan za ta gabatar da wani kuɗiri gaban majalisar dokokin ƙasar kan matakin korar jakadan Faransa.

Matakin ba zai kasance doka ba illa ƙoƙarin kwantar da tarzoma da hankalin ƴan jam’iyyar Islama ta TLP.

Ƴan jam’iyyar sun fusata kan yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna goyon baya ga ƴancin yin zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Gwamnatin Pakistan tana tattaunawa da jam’iyyar TLP kuma ta ce a shirye take ta janye tuhumar ta’addanci da ake yi wa fafutukarta.

Wasu shugabannin TLP, duk da haka, sun ce za su ci gaba da zanga-zangarsu, tare da shirin yin tattaki zuwa Islamabad da yammacin Talata.

A makon da ya gabata ne Firaministan Pakistan, Imran Khan, ya yi kira ga gwamnatocin ƙasashen yamma da su ɗauki mataki a kan mutanen da ke furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW, kamar yadda suke yi a kan waɗanda suka musanta kisan kiyashi da aka yi wa yahudawa.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *