Ramadan: Babban Malami, Kabiru Gombe ya yi kira ga Buhari, Gwamnoni da babbar murya

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi kira ga shugaban kasa da Gwamnoni – Malamin ya ba masu mulki shawara su fito da kudi, su taimaka wa al’ummarsu da binci.

Shehin ya ce hakan ne hanya mai sauki da za a bi, a kawo karshen masu satar mutane Fitaccen malamin addinin nan, Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya duba halin da al’umma su ke ciki.

A wajen darashin tafsirin da yake gabatar wa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban Najeriya ya buda baitul-malin gwamnati.

Kabiru Haruna Gombe ya bukaci shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohi su fito da kudi da nufin ba talakawa kayan abincin da za su ci a watan azumu.

“A bude baitul-mali, a saya wa talakawa tireloli na kayan abinci; shinkafa ta rika yawo, ana ba talakawa.”

“Ya ku gwamnonin jihohi, ku bude baitul-mali, a saya wa talakawa abinci a lokacin Ramadan. A fitar da dukiyar talakawa, a saya masu abinci saboda Allah.”

Shararren malamin kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah ya ba gwamnatin kasar shawarar yadda za a magance matsalar satar mutane.

Sheikh Gombe ya ce:

“Masu garkuwa da mutane sun addabe ku, su na ta kashe miliyoyi a kan tsaro domin ku tsare al’umma, amma har yau babu nasara.”

Ga hanya mai sauki da za ku yi nasara, ku ji tausayin na-kasa, idan ku ka yi haka, Allah zai ji tausayinku.”

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *