Rashin Janar Attahiru a Nageriya Koma baya ne a kokarinmu na Kawar da muggan Mutane ~Inji Sanata Uba Sani.

Rashin Janar Attahiru A Nageriya Koma baya ne a kokarinmu na Kawar da muggan Mutane daga Nageriya ~Inji Sanata Uba sani

Sanata Uba sani ya bayyana girgizarsa ga rasuwar Shugaban Sojojin Nageriya Janar Attahiru
Da ya ke bayyana alhininsa Sanatan Yana Cewa Labarin rasuwar babban hafsan sojan kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami’ai da ma’aikatan jirgin Saman a hatsarin wannan jirgin sama abu ne mai Matukar girgiza zuciya
kuma babban koma baya ne a kudurinmu na dakile miyagun mutane da suka yiwa kasarmu kawanya.

Laftanar Janar Attahiru yana kan gaba gaba tun lokacin da ya fara aiki a matsayin Shugaban hafsan sojan Nageriya domin ganin burinsa ya cika, Ya ci gaba da jajircewa duk da manyan kalubalen dayake Fuskanta, lallai Najeriya ta yi rashin jami’in kirki da Kuma kwazo.

Sanatan ya Kara da Cewa Ina mika ta’aziyata ga Iyalan Janar Attahiru da Shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari da Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Irabor, da Baki dayan Sojojin Nageriya, da kuma ‘yan Nijeriya baki daya. Allah ya gafarta kussakuran Laftanar Janar Attahiru ya kuma ba shi Aljanah Firdausi.

Ina mai mika sakon ta’aziyata ga danginsa da sauran jami’ai da ma’aikatan jirgin da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin. Allah yasa sun huta cikin cikakkiyar salama.

Sanata Uba Sani,
Gundumar Sanatan Kaduna ta Tsakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *