Rashin jituwa tsakaninta da ministan sufuri Rotimi Amechi shine alilin da yasa aka tsige Dr. Hadiza Bala Usman daga mukaminta.

Bayanan da suke shigowa yanzu game da sauke Dr Hadiza bala Usman daga mukamin ta Na shugabar NPA shine cewa akwai rashin jituwa da ke faruwa tsakanin ta da ministan sufuri Rotimi Amechi.

Bayanan sunce ministan sufuri Rotimi Amechi yasha kai karar ta wajen shugaba Buhari akan cewa bayajin dadin aiki da ita sakamakon wasu dabi’unta da bayaso.

Amma a nata bangaren Dr Hadiza bala Usman tace ba komai bane yasa ministan sufurin bayajin dadin aiki da ita illa kokarin da take Na ganin ma’aikatar tata ta fita hakkin kowanne bangare Na kasar Najeriya.

Za a saurari bayanin ministan sufurin Rotimi Amechi a gobe juma a donjin tabakinsa

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *