Rigimar ministan Sufuri Rotimi Ameachi da Hadiza Bala Usman a NPA yadauki wani Sabon salo.

Anyi watsi da zargin batar da kudi an koma zargin ta da rashin kunya, Babban zunubin Hadiza Bala Usman shine tana yiwa Ministan Sufuri Rotimi Ameachi rashin kunya.

Wani a cikin ‘yan kwamitin da aka kafa ya shaidawa manema Labarai cewa yanzu zasu maida hankali ne kan zargin ta da rashin kunya.

Yace yanzu ministan yayi watsi da zargin da yakeyi wa Hadiza Bala Usman Na kin dawo da Naira biliyan 165 asusun gwamnatin tarayya Na CFR.

Yakara da cewa yanzu suna kallon Abu biyu, Na farko Shugabar ta kasance tanayin magana da Shugaban kasa kai tsaye tana watsi da ofishin mai girma minista, yace Babban rashin kunya ne da saba tsarin dokar aiki, yace wannan ya isa yasa a tsigeta.

Na biyu ministan ya bata umarnin ta dawo da Kwangilolin Intel da aka dakatar. Abinda bata Sani ba shine har shugaban kasa yasan da maganar, batayi abinda aka umarce ta ba, wannan sabawa maganar manya ne, to batafi karfin a horas da itaba.

Wata majiyar kuma ta tabbatar da cewa Babban hadimin Shugaban kasa Farfesa gambari yataba aikawa da shugaban kasa wasika kan nuna goyon bayan sa ga Hadiza Bala Usman domin jin shawarar sa, saboda yana da yakinin Hadiza Bala Usman din tafi ministan gaskiya.

Wani Karin aiki da kwamitin da aka kafa zaiyi shine, binciken kwangilolin da NPA ta bada, Wanda a doka ministan ne keda hurumin sa hannu kafin a fitar da manyan ayyuka ba Shugabar NPA Hadiza Bala Usman ba.

Sauran bayani Na nan tafe.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *