Rikicin PDP a Arewa Maso Yammah Laifin Kwnakwaso ko Tambuwal?

A jiya Asabar ne aka tashi Baram-Baram a zaben shugabannin Jam’iyyar PDP shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya da akaso Gudanarwa a Jihar Kaduna har takai ga an dage zaben zuwa wani lokaci.

Tun bayan bullar wancan Rikici maganganu suke ta yawo akan mutum biyu wato tsohon gwmanan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa kwnakwaso da Kuma gwamnan Jihar Sokoto Rt.Hon Aminu Waziri Tambuwal sune Musababbin haifar da dukkan wata hatsaniya a Jam’iyyar PDPn shiyyar Arewa Maso Yamma.

To a iya Binciken Dana gudanar na gano ainihin Musababbin Abunda ya faru a dangane da wannan tirka tirka Kuma Zan faiyyace muku ita yanzu yanzu.

Kamar dai yadda yake Rubuce a kundin tsarin Mulkin Jam’iyyar PDP ita shiyyar Arewa Maso Yamma wato Northwest Zone da suka hada Jihohi guda 7 Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano Kebbi,Sokoto da zamfara tana da tsarin shugabanci na mutu 17;
ZONAL VICE CHAIRMAN
ZONAL SECRETARY
ZONAL P.R.O
ZONAL YOUTH LEADER
ZONAL ORG.SEC
ZONAL TREASURER
ZONAL LEGAL ADVISER
ZONAL FINANCIAL SEC
ZONAL AUDITOR
ZONAL WOMEN LEADER
ZONAL EX-OFFICIO 1
ZONAL EX-OFFICIO 2
ZONAL EX-OFFICIO 3
ZONAL EX-OFFICIO 4
ZONAL EX-OFFICIO 5
ZONAL EX-OFFICIO 6
ZONAL EX-OFFICIO 7
Wadannan shugabanni za’a rabasu ne gida 7 ko wacce jiha ta dauki nata ta hanyar zaman tattaunawa da Jagororin Jam’iyyar na wannan shiyya sannan Kuma daga bisani ko wanne jagoran Jam’iyya ya koma Jiharsa ya zauna da Mutanensa su fito da wadanda za’a bawa Mukaman Kuma hakan shine ya faru a wannan shiyya ta Arewa Maso Yammah.

A ranar 4/4/2021 Jagororin Jam’iyyar PDP shiyyar Arewa Maso Yammah sunyi wata ganawa a gidan tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Maigirma Attahiru Dalhatu Bafarawa dake Abuja inda anan ne aka raba wadannan Mukamai guda 17 a kabawa ko wacce Jiha nata Kuma kowa ya amince da hakan Babu Wanda yayi korafi ga yadda rabon ya kasance Kamar haka;

JIGAWA
Zonal PRO
Zonal Ex-officio

KADUNA
Zonal Secretary
Zonal Legal Adviser
Zonal Ex-officio

KATSINA
Zanal Treasurer
Zonal Ex-officio

KANO
Zonal Vice chairman
Zonal women leader
Zonal Ex-officio

KEBBI
Zonal Org-Sec
Zonal Ex-officio

SOKOTO
Zonal youth leader
Zonal Auditor
Zonal Ex-officio

ZAMFARA
Zonal financial Secretary
zonal Ex-officio

Bayan kammala wannan taro an bawa ko wanne Jagora fama-famai na Jihar sa ya rabawa Yan takarkarun da zasu zabo sai su cike a mayar shalkwatar Jam’iyya dake Kaduna, to inda matsalar ta kunno Kai shine shi Gwmanan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal sai ya tsallaka Jihar Kano yace ala Dole sai ya tsaida Dan takarar Zonal vice Chairman nasa na kansa Wanda Kuma wannan ba hakkinsa bane hakki ne na Jagororin Jam’iyya na Jihar Kano tunda Babu inda akace wani Jagora ya shiga wata Jihar da ba tasa ba yayi katsalandan Kuma Tambuwal yayi hakane ta hanyar hada Kai da wasu Jagororin Jam’iyyar na Jihohin Jigawa,Zamfara, Kebbi da sauransu hakan tasa shikuma Jagoran Jam’iyyar PDP na Jihar Kano Rabi’u Musa kwnakwaso yace bazata sabuba Bindiga a ruwa yadda bai shiga wata Jiha ya tsayar musu da Dan takara ba to Babu wasu Jagorori na wasu Jihohi da zasu shigo Jihar sa su tsayar masa da Dan takara.

Jiya Asabar 10/4/2021 itace ranar da aka saka domin taruwa a kasuwar Bajakoli ta Kaduna domin tabbatar da Kuma rantsar da wadannan shugabanni da Jagororin Jihohi zasu kawo to Abun mamakin shine ko wacce Jiha ta gabatar da mutum guda daya akan ko wacce Kujera da aka bata amatsayin Wanda yake takara ma’ana shi kadai za’a kadawa kuri’a yaci Babu hamayya sai Jihar Kano ita kadai ce aka gabatar da Mutum biyu Hon. Yusif Jamo dakuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo amatsayin wadanda suke Takara akan Kujerar Zonal vice Chairman ma’ana Dan takarar Kwankwaso da Dan Takarar Tambuwal, wannan shine dalilin da yasa Magoya bayan Sanata Rabi’u Musa kwnakwaso suka kekasa kasa sukace lallai hakan bazai yiwu ba Dole ne kamar yadda ko wacce Jiha ta gabatar da Mutum daya a kan ko wcace kujera to suma a karbi nasu Mutum guda din amatsayin Dan takara daya tilo wanda zaici Babu hammayya kamar yadda yake cikin yarjejeniyar da akama cimma ranar 4/4/2021 gidan Bafarawa idan Kuma ba haka ba to saidai a dage wannan zabe na yau idan yaso abawa kowanne Jagora Dama ya shiga ko wacce Jiha ya tsayar da Dan takara kamar yadda Tambuwal yazo Kano ya tsayar da Dan takara, haka dai guri ya hargitse aka faffasa akwatuna zabe aka yayyaga takardun kada kuria’a Abunda tilasta Jagororin Jam’iyyar suka fice daga wurin Baturen zabe Kuma daga Hukamar Zabe ta kasa INEC ya dage zaben gaba daya.

Wannan shine ainihin Abunda ke faruwa ko Kuma nace ya faru da Jam’iyyar PDP shiyyar Arewa Maso Yammah duk wanda ya fada muku wani Abu sabanin wannan to yayi muku karya,

To yanzu Laifin Kwnakwaso ne ko Tambuwal?

Daga Khadija Garba Sanusi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *