Labarai

RIKICIN PDP: Na zabi na koma gefe nayi shiru da bakina ne domin yanzu ba Lokacin magana bane ~Cewar Bukola Saraki.

Spread the love

Tsohon shugaban majalisar dattijan Nageriya Abubakar Bukola Saraki ya bayyana hakane a shafin sa na Facebook Yana Mai cewa A cikin makon da ya gabata na dawo daga hutun ƙarshen shekara da na saba zuwa, kaitsaye na wuce Jihar Akwa Ibom domin halartar taron cika shekara 35 da kafa jihar.Yayin da na zagaya wasu sassan ƙasar nan a ‘yan kwanakin nan, na fahimci cewa mutane da yawa sun damu da shiruna kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyarmu ta PDP. A tawa fahimtar, akwai lokacin yin magana, akwai kuma lokacin da mafi dacewa shi ne ka yi shiru ka yi ta yin aiki abinka a bayan fage. Yanzu shi ne irin wannan lokaci. Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar sune mafi dacewa a zaɓa a zaɓen 2023. Inji shi.Sanata Bukola Saraki na daya daga cikin wa’yanda suka nemi jam’iyar PDP da ta Basu Tikitin tsayawa takara na matakin shugaban kasa Amma Atiku Abubakar ya kifar dasu a Lokacin zaben Fidda Gwani na jam’iyar jama’a da dama na ganin cewa shirun da Bukola Saraki yayi na da nasa da rikicin dake faruwa tsakanin Atiku da Wike Lamarin da Saraki ya karyata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button