Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina tayi Nasarar chafke ƙauraye, Mai Fyade da kuma Ɗan Damfarar ATM…

Da yake bayyana wadanda ake zargin Mai Magana da yawun Rundunar Ƴansandan ta jihar Katsina SP Isah Gambo yace an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban daban cikin birnin Katsina wadanda aka samu da ganyen Tabar Wiwi, Sholusho, Adda, Layu da sauran su.

Ƙaurayen dai da aka kama sun had’a da

  1. Hafiz Iliyasu 2. Abubakar Habibu 3. Nura Lawal 4. Aliyu Yusuf 5. Umar Sani 6. Imrana Abubakar 7. Muhammadu Sabo 8. Ismaila Sanusi 9. Ibrahim Abdulmalik 10. Ibrahim Habibu dukkanin su Ƴan Shekaru tsakanin Ashirin 20 zuwa Ashirin da Biyar 25 da suke zaune a wurare daban daban cikin Katsina.

Kazalika Rundunar ta kama wani Abdulkadir Abdulkarim, Ɗan kimanin Shekaru Hamsin 50 daga ƙauyen Ɗauki, cikin ƙaramar Hukumar Batsari amma yanzu yake da zama a Unguwar Modoji dake cikin garin, Katsina, wanda aka samu da laifin yima ƙananan Yara fyade, kama daga Shekaru Ukku 3 zuwa Biyar 5.

Da ake binciken shi wanda ake zargin yace yana amfani da yatsan shine wajen lalata da Yaran.

Haka nan kuma an kama wani Matashi da ya ƙware wajen damfarar Mutane ta hanyar yaudarar su yayin da sukazo neman kuɗi wajen Injin bada kuɗi ATM, Matashin Aliyu Abdullahi, Ɗan kimanin Shekaru Ashirin da Ɗaya 21 daga Unguwar Kasuwar Maya ƙaramar hukumar FUNTUA.

Aliyu ya bayyana yadda yake yaudarar Al-umma yayin da sukaje amfani da ATM ya kuma bayyana cewa yana zuwa bankuna tsakanin UBA da First Bank da suke kan hanyar IBB way, Katsina.

Yace yakan tsaya ne bakin Bankin ya jiya wanda ATM din yaƙi amsar katin shi sai yazo da niyyar taimakawa daga nan ne sai ya canza maka da katin ATM na bogi ya tafi da naka zuwa wani bankin ya cire kuɗin dashi.

Ya kuma ƙara da cewa a’kallah ya kwashi kudin Mutane Naira Milyan Ɗaya da Dubu Ɗari Shidda da Shidda da Ɗari Hudu (6,606,400, 000) daga Asusun kimanin Mutane Shidda (6) da suka faɗa komar shi.

Jami’an tsaron suna cigaba da bincike akan dukkan wadanda ake zargin.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *