Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta sun dakile harin da Boko Haram yan Boko Haram suka kai a Dikwa

Yan Boko Haram sun ji ‘ba daɗi’ a hannun sojoji yayin da suka yi yunƙurin ƙwace Dikwa

Rundunar sojojin ta ce dakarunta sun kashe yan Boko Haram da dama tare da lalata musu makamai da motocci

Mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Manjo Janar Mohammed Yerima ne ya bada sanarwar

Dakarun sojojin Nigeria, a ranar Lahadi sun dakile yunkurin da yan Boko Haram suka yi na kwace iko a garin Dikwa, hedkwatan karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

Sanarwar ta mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria, Mohammed Yerima ya fitar a Twitter ta ce yan ta’addan da dama sun mutu a yayin harin da suka yi yunkurin kai wa.

Daga Ahmad Aminu Kado..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *