Labarai

Rundunar ‘yan sanda ne ke kawo Mana tashin hankali a cikin siyasa Lokacin zaben jihar Kano ~Cewar Abba Gida-Gida.

Spread the love

Ɗan takarar na gwamnan kano a jam’iyyar NNPP Abba K Yusuf yace ƴan sanda ne abin zargi game da ƙaruwar tashe-tashen hankula na siyasa a jahar ta kano.

Ɗan takarar ya bayyana hakan ne yau a taron tabbatar da zaman lafiya a jahar kano wanda hukumar ƴan sanda ta jaha haɗin gwiwa da Gidauniyar AMG da wasu ƙungiyoyin na al’umma a ƙarƙashin inuwar G31.

Cikin bayanan mai magana da yawun sa Hon. Sunusi bature dawakin tofa ya fitar, Abba Gida-Gida yace jam’iyyun adawa a Kano sun haɗe kawunan su game dukkan wani nau’i na ɓatanci da cin zarafi na jam’iyya mai mulki APC, yayi bayanin cewa suna amfani da wani salo wajen cin zarafin zaɓaɓɓu a cikin al’umma.

Ya bayyana yanda hare-hare na tashin hankali da shugaban jam’iyyar APC na jiha Abdullahi Abbas da ɗansa Sani Abdullahi Abbas da akafi sani da (Ochi) suka shirya.

Ɗan takarar gwamnan na NNPP ya ƙara da cewa har sai hukumar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro sun shirya yin aikin da ya dace da ƙwarewarsu tare da haƙiƙanin gaskiya, a ƙyale al’ummar kano sun binciko hanyoyin kare kai kamar yadda akayi tanadi cikin kundin doka na tarayyar Nigeria.

“Mun ga yadda wasu jami’an ƴan sanda suka goyi bayan hare-haren tashin hankalin ƴan ta’addar siyasar APC, an farmaki tawagata da kuma gidan ahali na dake Chiranci a ƙaramar hukumar Gwale shima sun farmaka, duba da tarin ƙorafe-ƙorafe da na rubuta, babu wani mataki da aka ɗauka har yau”.

Abba Gida-Gida ya tabbatar da jajircewarsa da na jam’iyyarsa NNPP, zasu bada dukkanin haɗin kai domin tabbatar da sahihi, ingantaccen zaɓe na gaskiya ba tare da wata matsala ba a 2023 idan har jami’an tsaro da ma’aikatan zaɓe ba su kasance masu son zuciya ba.

A amsar gaggawa, Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano, CP Mamman Dauda ya nanata irin shirin da yayi na yin aiki da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar zaman lafiya kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

A lokacin bayanan rufe taro a madadin haɗakar ƙungiyoyin al’umma, Dr. Aminu Magashi Garba wanda shine wanda ya samar da gidauniyar AMG ya tabbatar da yunƙurinsu na ganin zaman lafiya da tsaro sun samu yayin gabatar da ayyukan zaɓe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button