Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Zamfara ta cafke wani likita da wasu mutane bakwai bisa zargin taimakawa da yan bindiga a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Gusau a ranar Alhamis, inda ya ce an cafke likitan ne a kauyen Kamarawa na karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Kwamishinan ya ce, mutanen da ke aikin Puff Adder ne suka cafke likitan saboda zargin ya ba da kayan soja ga ’yan ta’adda, kuma bayan bincike na farko, an kwato takalman shiga daji na sojoji guda goma, da singers biyar da kuma safunan hannu ta sojoji.

Dosara ya ci gaba da bayanin cewa biyu daga cikin bakwai din, wadanda ake zargin jami’an tsaro ne, an gudanar da bincike a kansu, sun amsa kansu da kansu cewa suna da hannu dumu-dumu awajen dakule ayyukan sojoji da yawa a jihar.

Ya kara da cewa wadannan wadanda ake zargin, a cewar su, sun yi aikin raba bayanan sirri na sojoji, da samar da makamai da alburusai, kayan sojoji da sauran kayan aiki ga ‘yan ta’adda da ke fadin jihar.

An kuma kama wani da ake zargi da hada baki da ‘yan fashin da kuma ba su alburusai, Dosara ya kara da cewa wasu jami’an’ yan sanda sun kama wani da ake zargi daga Sokoto saboda ya ba da kakin soja da kayan sawa ga wadanda ake zargin.

Ya kara da cewa “an gano military bulletproof guda 9 , kayan sawa guda hudu, safunan hannu na sojoji guda biyar, katin ATM na first bank guda biyu, katin ID na sojojin Najeriya daya da wayar hannu kirar kamfanin Samsung daya a hannun wanda ake zargin .

Ahamd Aminu Kado…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *