Samar da Dokar bankin Islama Sheikh Dr Bashir Alfurqan ya Jinjinawa Sanata Ub.

A makon daya gabata ne Shugaban kasa Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan kudirin doka na kafa bankunan Musulunci da kasuwanci da hada-hadar kudade a Najeriya bayan tsawon lokacin da aka kwashe ana tsumaye.

Wannan kudiri ne wanda Sanata Uba Sani mai wakiltar Jihar Kaduna ta tsakiya a zauren Majalisar Dokoki, ya jagoranta kuma har ya tsaya tsayin daka kudirin ya sami tabbacin gudanarwa.

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Dakta Bashir Alfurqan, ya ce wannan aikin Alkairi ne wanda ya kamata Al’ummar Musulmai su yayata duniya ta sani, ya yi alfahari da wanda suka jagoranci tabbatar da wannan alkairin musamman Sanata Uba Sani, inda yayi mishi Adduar samun Aljannah.

Sanata Uba Sani ya kawo kuduri wanda ya jawowa Musulman Najeriya dama duniya babban ci gaba,domin kuwa doka ce wacce ta tabbatar tare da jaddada Bankunan Musulunci da sauran kamfanonin hadar hadar kudade a Musulunce.

Yanzu haka Mutane da dama wanda suke da burin zuwa su kafa bankunan Musulunci a Najeriya, tsoron rashin tabbatar da dokar ne ya hana su amma yanzu zasu zo don tabbatar hakan don Musulunci ya sami tagomashin amfana da tattalin arzikin kasa; inji Dr Bashir

Leave a Reply

Your email address will not be published.