Sanata Uba Sani Shine Sanata na farko daya fara kafa wannan Dabi’ar ta daraja bil’adama a tarihin jihar kaduna.

Bayan ya lashe Zaben kujerar Zama Sanata Mai wakiltar kaduna ta tsakiya Yaci gaba da kusantar Al’ummar daya ke wakilta domin share masu hawayen su, idan baku manta ba Zaku iya tuna yadda sanatan ya Ke Kai Ziyarar daurin aure tare da Ta’aziya rasuwa ga talakawan dayake wakilta Misali sanatan yakai ziyarar Ta’aziya Ga Iyalan Alhaji Tijjani Abubakar Bisa Rasuwar Dansa, Aliyu Tijjani, malamin Makaranta Kuma Dan Asalin jihar Kaduna, Wanda Aka Yiwa Duka aka kashe shi a Bishket da sauransu wa’yanda baza su lissafu ba.

Idan baku manta ba A Ranar 2 ga watan Yulin na 2019 ne Fitaccen Sanatan Ya Shirya wani Zama Tare Da Tawagar APC Social Media Inda Ya Karbi Bakuncin Yan Social Media din Sama da mutun dari biyu 200 domin nuna Godiya a gare su da Kuma Yi musu Nasihar fahimtar dasu Karfin da Kafafen Yada Labaran Zamani ke dashi da Kuma Basu karfi da Cigaba da tallata kyawawan Ayyukan Gwamnatin su ta apc musamman Gwamnatin jihar kaduna karkashin Jagoranci Malam Nasiru El Rufa’i bisa doron da’a da Dabi’ar gaskiya.

Ya cigaba Sanatan ya kuma karbi bakuncin taron masu ruwa da tsaki tare da shugabannin kungiyar, Dattawan yankin da shugabannin addinai daga karamar hukumar Giwa domin Zuwa ziyarar godiya gare shi bisa Kudirin daya Tallafa ya kai masu domin Kafa Kwalejin Ilimi A Karamar Hukumar ta Giwa.

Abin mamaki ne ga Dan Majalisa ace bayan yaci zabe Kuma a sake ganin sa yana yawo mazabu mazabu wai domin godiya ga Al’ummar da suka zabe shi Malam Uba Sani bayan lashe Zaben kujerar Sanata tsakanin Rana ta 8 zuwa 15 na Watan Satumbar 2019, Fitaccen Sanatan ya fara rangadin ziyarar Godiya zuwa Kananan Hukumomi Bakwai (7) da yake wakilta Kuma ya bi su gari gari Yana Mai godiya a gare su Kan zabensa da sukayi ya Zama Sanata, hakika faruwar irin wannan Dabi’a ta ganin darajar al’umma ga dan siaysa wannan shine Karo na farko a tarihin jihar kaduna…

Leave a Reply

Your email address will not be published.