Labarai

Sanata Uba sani Ya kaddamar da littafi akan Naira Milyan goma 10m.

Spread the love

Sanata Uba Sani ya sanar da hakan a cikin wani saƙo daya fitar ga Manema kabarai Yana cewa a yau, na ji daɗin kasancewa Babban Mai Gabatarwa kuma Mai ƙaddamar da littafin mai suna: “Fundamentals Of Geoscience” na ɗan’uwana kuma abokina, Farfesa Matoh Dary Dogara wanda na san shi kuma na yi aiki da shi tsawon shekaru da dama”

A cewar Uba Sani, wannan taro wanda ya samu halartar wasu fitattun mutane daga jihar Kaduna da wajenta, ya ƙunshi Malaman Jami’o’i daga sassan kasar nan ya ba shi damar yin magana kan mahimmancin ilimin kimiyyar kasa, da ya shafi muhalli.

Ya kuma yabawa wanda ya rubuta littafin, inda yace babu shakka yana ɗaya daga cikin haziƙan masu hankali da suka fito daga jihar Kaduna.

Bayan gabatar da jawabi, Sanatan ya gabatar da bikin kaddamar da littafin a hukumance wanda ya ƙaddamar dashi akan kudi naira miliyan goma (N10,000,000).

“Domin tallafa wa wannan gagarumin aiki da dan uwana ya yi ta hanyar sayen kwafin littafin da za a raba a makarantu daban-daban a fadin Kaduna.

Yace “Ina ba da shawarar littafin da aka rubuta da kyau ga cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin muhalli, masu bincike, masu fafutukar sauyin yanayi, malamai da duk waɗanda ke neman samun amsoshin ilimin kimiyyar ƙasa na zamani dasu Kasance da wannan littafi”.

Sanata Uba sani shine Dan takarar Gwamnan jihar kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC Mai alamar tsin-tsiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button