
A wani kokarin sa na martaba tsarin addinai Sanata Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Malam Uba sani ya bi Coci-Coci da Masallatai na duk Kananun hukumomi bakwai 7 da yake wakilta ya kafa fitilu masu anfani da Hasken Rana (SOLAR) a Duk kokarin da yake domin farantawa tare da Cika Alkawarin daya dauka ga jama’arsa..
Sanata uba sani na Cigaba da kawo cigaba a Yankinsa na kaduna ta tsakiya dama jihar kaduna Baki daya Sanatan ya ciri tuta wajen Ayyukan alkhari idan baku manta ba a makon Daya gabata ne Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El’rufa’i ya Jinjinawa kokarin na Sanata uba sani bisa kawo Ayyukan alkhari ga Jihar kaduna…