Sanusi Lamido Na II ya Jinjinawa Ganduje bisa matakin daya dauka Kan Sheikh Abdujabbar.

A wani bidiyon da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido Na II ya fitar ya nuna Goyon bayansa ga Gwamnatin Jihar kano bisa matakin data dauka Kan Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara na hanashi karatu

Sarkin Yace jama’ar Kano a cigaba da tsayawa, a cigaba tsayawa, akan cewar mu Kano bazamu tsaya akan komai ba sai abinda Shehu Usmanu Danfodiyo ya dora mu akai, shine Aqeedar Ahlussunah Wal-jama’a.

Kuma dukkanin mutumin da zaizo kowaye ne shi, ya fito mana da wani abu daban ya kamata mu nuna masa cewa Kano bazata zama Markazee na wanna ba, kuma Malaman Kano kun kyauta a cigaba da abinda akai, kuma a cigaba da zama da zama lafiya, sannan kuma wannan mataki da Gwamna ya dauka ya matakai ne da ya kamata a yaba musu akai kuma a goya musu baya”

~ Sarki Sanusi II

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *